1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kashe 'yan tawayen Burundi

November 27, 2022

Kimanin 'yan tawayen Burundi guda 40 ne aka halaka a wani artabun da suka yi da sojojin Jumhuriyar Dumukuradiyyar Kwango da na Burundi a gabashin Kwango.

https://p.dw.com/p/4K9rt
Sojojin Burundi
Sojojin BurundiHoto: Mohamed Abdiwahab/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Kwango ce ta sanar da haka a Lahadin nan, tana mai cewa wani atisayen hadin gwiwa na kasashen biyu ne ya kutsa kai har maboyar 'yan tawayen kuma ya yi nasara a kansu.

Sojojin Kwangon a cikin wata sanarwa da suka fitar sun bukaci matasan yankin Kivu, inda lamarin ya faru da su yi kokarin nesanta kawunansu da 'yan tawayen na kan iyaka.

Tun dai a watan Agustan da ya gabata, sojojin Burundi ke aikin samar da tsaro a gabashin Kwango a matsayin wani bangare na aikin samar da zaman lafiya na kungiyar kasashen gabashin Afirka.