1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun hallaka shugaban kasar Hait

July 7, 2021

Rahotannin daga kasar Haiti na nuna cewa da sanyin safiyar ranar Laraba, wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun harbe shugaban kasar Jovenel Moise har lahira.

https://p.dw.com/p/3wA5g
Haiti Präsident  Jovenel Moise
Hoto: Dieu Nalio Chery/AP Images/picture alliance

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Mininstan cikin gidan kasar Claude Joseph ya ce maharan sun kai harin ne gidan shugaban kasar mai shekaru 53 da misalin karfe 1 na daren Talata kuma mai dakin shugaban kasar ta ji mummunar rauni inda take kwance a asibiti.

Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ya dabaibaye kasar dake jerin kasashen Caribbean. Kuma ayyukan agaji ke fuskantar barazana yayin da ake fama da karancin abinci a kasar. Wutar rikicin ya kara ruruwa ne bayan da talauci ke neman yiwa kasar katutu wanda ya haifar da gudanar da jerin zanga-zanga tun bayan da marigayi Moise ya hau karagar mulki a shekarar 2017. A wannan shekarar ce dai 'yan adawa a kasar suka zargi shugaban da mulkin kama karya, zargin da ya musanta.