Kwango: Madugun adawa ya gaza shiga kasar
August 3, 2018Talla
Shi dai Mr. Katumbi wanda hamshakin dan kasuwa ne, an dakatar da shi daga shiga kasar ne a kan iyakar kasar da Zambiya. Dan siyasan wanda tsohon gwamna ne a yankin Katanga, na zaune ne a kasar Beljiyam tun cikin watan Mayun shekara ta 2016, bayan takaddama tsakaninsa da Shugaba Joseph Kabila.
A wannan makon ne ma wani babban mai adawa da Shugaba Kabilan wato tsohon mataimakain shugaban kasa Jean-Pierre Bemba ya koma kasar ya kuma bayyana takararsa ta shugabancin kasa a ranar Alhamis da ta gabata. Shi dai Shugaba Joseph Kabila na jagorantar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ne tun a shekara ta 2001.