1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Soji sun haramta zanga-zanga a Burkina faso

Abdoulaye Mamane Amadou
October 27, 2023

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta haramta gudanar zanga-zangar kin jinin matakan hana walwala da take kakabawa al'ummar kasar

https://p.dw.com/p/4Y8Es
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim TraoreHoto: Alexey Danichev/AFP

Hukumomi a Burkina Faso sun haramta gagarumar zanga-zangar ne bisa hujjar rashin tabbataccen tsaro da kasar take fuskanta

A cikin wani sakon da ya aike wa kungiyoyin da suka shirya boren na ranar Talatar da ke tafe, babban magajin garin birnin Ouagadougou Maurice Konaté, ya bukaci da su jingine zanga-zangar har sai lokacin da tsaro da kwanciyar hankali suka sake tabbata a kasar ta yammacin Afirka, mai fama da hare-haren 'yan ta'adda.