1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramta zanga-zanga a Togo

Suleiman Babayo
December 6, 2018

Gwamnatin Togo ta haramta zanga-zanga yayin da aka fara yakin neman zaben shiga majalisar dokoki inda 'yan adawa suka ce ba za shi zaben ba.

https://p.dw.com/p/39aN1
Togo Demonstrationen
Hoto: DW/N. Tadegnon

Gwamnatin Togo ta haramta duk wata zanga-zanga da 'yan adawa suka tsara bisa dalilan tsaro. Gamayyar jam'iyyun adawa 14 suka bayyana niyyar janyewa daga zaben 'yan majalisa da aka tsara ranar 20 ga wannan wata na Disamba maimakon haka suke neman an katse komai domin tabbatar da gyare-gyare ga tsarin. Sai dai tuni aka kaddamar da yakin neman zabe.

Shugaba Faure Gnassingbe yana rike da ragamar mulkin kasar ta Togo da ke yankin yammacin Afirka tun shekara ta 2005 shekaru 13 ke nana, kuma ya gaji mulkin daga mahaifinsa Gnassingbe Eyadema wanda ya shafe shekaru 38 kan madafun iko. Shugabannin kungiyoyin Kiristoci masu shiga tsakanin sun bukaci gwamnatin ta Togo ta jinkirta zaben na 'yan majalisar dokoki.