Nijar: An hana 'yan adawa zanga zanga
March 19, 2021Talla
Cikin sanarwar da ya fitar, babban magajin garin Yamai yace ya dauki matakan hana zanga-zangar ne, saboda yiwuwar samun tada zaune tsaye a yayin gangamin, kana kuma da fargabar yaduwar annobar corona.
Jam'iyyun na adawa sun bayyana cewa za su ci gaba da jajircewa har sai an tabbatar da dan takarar jam'iyyun adawa Mahamane Ousmane a matsayin shi ne ya lashe zaben
Zanga-zanga dai ta barke jim kadan bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da Bazoum Mohamed a matsayin wanda yayi nasarar zaben na ranar 21 ga watan jiya, tare da sanadin mutuwar mutun biyu, baya ga wasu daruruwan mutanen da aka kama ciki har da tsohon madugun 'yan adawa Hama Amadou.