1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbo jirgin sojin Ukraine a Slovyansk

May 2, 2014

Mahukuntan Ukraine sun ce 'yan awaren da ke rikici da gwamnati sun harbo wani jirgin yakin Ukraine din a yankin na Slovyansk da 'yan aware ke rike da shi.

https://p.dw.com/p/1BsG9
Ukraine Unruhen in Slowjansk 24. April
Hoto: Reuters

Ministan cikin gidan Ukraine din Arsen Avakov ya ce tuni matukin jirgin ya rigamu gidan gaskiya sakamakon fadowar jirgin wanda na soji.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da shugaban Amirka Barack Obama da shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel da ke ziyara a Washington za su tattauna a yau kan halin da ake ciki a kasar Ukraine.

Zantawar tsakanin shugabannin biyu dai wadda za ta wakana a fadar White House ita ce ta farko tsakaninsu tun bayan da rikicin Ukraine ya barke jim kadan bayan da Rasha ta maida yankin Kirimiya mallakarta a watan Maris.

Kafin tafiyarta zuwa Washington dai, Angela Merkel ta sake jaddada kiranta ga shugaban Rasha Vladimir Putin domin ya taimaka game a sako wakilan hukumar tsaro da hadin kan Turai wato OSCE da 'yan tawayen na gabashin Ukraine suke garkuwa da su.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu