1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Turai ta daina dogaro da makamashin Rasha

Ramatu Garba Baba
March 10, 2022

A gabanin wani taron kasashen Kungiyar Tarayyar Turai, Shugaba Emmanuel Macron ya bukaci Turain da ta san yadda za ta rage dogaro kan iskar gas daga Rasha.

https://p.dw.com/p/48Jox
Frankreich Russland-Ukraine-Krieg EU-Gipfel Schloss Versailles
Hoto: Michel Euler/AP/picture alliance

Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen da ke Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da su tsayar da matsaya a game da yadda za su bullo wa harkar cinikin  man fetur da iskar gas a tsakanin su da Rasha. 

Macron ya fadi haka ne a yayin da yake magana a wannan Alhamis, gabanin taron Kungiyar EU a Faransa. Sai Macron ya yi wa Kungiyar EU gargadi a game da sanya kasar Ukraine cikin mambobinta, inda ya ce, ba abu ne mai yiwuwa a yi wa kasar da ke cikin yaki rajista a kungiyar ta kasashen Turai ba. Ana ci gaba da gwabza yaki a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine inda rayuka da dama daga bangaren Ukraine suka salwanta baya ga wasu sama da miliyan biyu da suka rikide zuwa 'yan gudun hijira.