An janye jirgin da ya rufe mashigar Suez
March 29, 2021Talla
Hukumomimn kasar Masar sun tabbatar da janye jirgin dakon kayan da ya toshe mashigar ruwan Suez kusan mako guda, matakin da ke sa fata mai kyau na budewar hanyar kasuwancin kasar nan ba da jimawa ba.
Mashigin ruwan na Suez, wanda ya hada Bahar Rum da tekun Maliya wato Red Sea, ya kasance kashin bayan harkokin sufurin teku na kasa da kasa tun bayan da amincewar jiragen ruwa su gudanar da zirga-zirga tsakanin kasashen Turai da kudancin Asiya ba tare da zagaye nahiyar Afirka ba.