1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kada kuri´ar rashin amincewa da gwamnati a Ukraine

January 10, 2006
https://p.dw.com/p/BvCq

Majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri´ar sallamar gwamnatin FM Yuri Yekhanurov. An gabatar da kuri´ar rashin amincewa da gwamnatin ne bayan yarjejeniyar da birnin Kiev ta kulla da Mosko a makon jiya, wadda a ciki Ukraine ta amince ta saye iskar gas daga Rasha akan farashin da ya rubanya na bara har sau biyu. Wakilai 250 na majalisar dokokin mai kujeru 450 suka goyi bayan kuri´ar rushe gwamnatin. To sai dai Yukhanurov zai ci-gaba da rike wannan mukami har sai shugaba Viktor Yushchenko ya nada magajinsa. A cikin watan maris ake shirin gudanar da zaben ´yan majalisar dokoki a Ukraine.