1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hong Kong: An kafa cibiyar tabbatar da tsaro

Abdoulaye Mamane Amadou
July 8, 2020

China ta kaddamar da wani ofishin tsaro da ka iya baiwa jamian leken asirin kasar damar zartar da aiyukansu a yankin Hong Kong yini daya bayan soma aiki da dokar tsaro mai cike da cece-kuce.

https://p.dw.com/p/3ewNv
Hongkong Eröffnung Nationales Sicherheitsbüro
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Hong Kong Government Information Services

Da ta ke jawabi a yayin bikin kaddamar cibiyar tsaron jagorar yankin Carrie Lam, ta bayyana matakin a matsayin wani irinsa na tarihi, da ka iya taimakawa wajen tabbatar da tsaro da doka da oda da suka sukurkuce a yankin.

Shedun gani da ido sun tabbatar wa manema labarai hango alamomin China a wani hotel da ke dab da dandalin da masu zanga-zangar rajin girka dimukuradiya a yankin suka fi yawan taruwa, lamarin da masu adawa da sabon tsarin dokar ta China ke yiwa kallon wani sabon salo ne da ka iya rage karfinsu na fitowa don nuna adawa da dokar.