An kai hari a jami'ar Bayero ta Kano
April 28, 2012A ƙalla mutane 20 suka mutu yayin wani harin da aka kai a jami'ar Bayero ta Kano. Kamfanin dillalcin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kai harin ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da ibada wanda aka sabayi a babban dakin karatu na tsohowar BUK da safiyar yau. Rundunar soji dama jami'an yan sanda a birnin Kano sun tabbatar da kai harin, amma basu bada adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba kawo yanzu. Jami'ar Bayero dai tana da tsauraren matakan tsaro, domin a faɗar wani malami a jami'ar, idan mutun yaga irin binciken ƙwaƙwab da ake yi tun da ga ranar Juma'ar shekaran jiya, to zai yi mamaki ace mahara ɗauke da bama-bamai da bindigogi su samu shiga. Ganau suka ce maharan sun shiga da babura biyu da mota, inda suka fara buɗe wuta kan jama'a. An dai ji tashin bama-bamai da bindigogi tunda daga wajen jami'ar. kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.
Gabanin harin kan jami'ar Bayero
Hankali dai na dada tashi kuma zuciya tana shirin baki ga masu farautar labarai a tarrayar nigeria dake cikin tsaka mai wuya kuma ke kara fuskantar matsin lamba a kokarinsu na sauke nauyin aikin. A tsakanin gwamantin kasar da kuma yayan kungiyar boko haram din da suka kaddamar da wasu jerin hare hare akan kafafen yada labaran kasar 3.
Babu dai zato ba kuma tsammani aka wayi gari da hari kan wasu kafafen yada labaran kasar ta Najeriya uku a wani abun dake zaman sabon yanayi a cikin yakin ta'addancin da yaki ci yaki cinyewa kuma ke neman tsallakowa ya zuwa ga yan jaridar kasar ta Najeriya. Tuni dai kungiyar Boko haram mai fafutuka da boma bomai ta dauki alhakin shirin day a kai ga asarar rayuka akalla shida sannan kuma ya kai ga lalata offishin jaridar Thisday mai zaman kanta a nan Abuja. Kuma babbar hujja ta kai harin a cewar kungiyar na zaman rawar jaridun da rashin adalcin ga yanda suke baza labaran harkokin yakin ta'addancin kasar ta Nigeria.
Kungiyar dai na barazanar cigaba da kaddamar da harin kan kafafen yada labarai a cikin kasar ta Najeriya in har babu sauyin rawa a cikin abun da suka kira son raid a rashin adalci a cikin harkokin jaridun kasar ta Najeriya. Sabon harin dai na nuna irin jan aikin dake gaban mafarauta labaran kasar ta Najeriya dake tsaka mai wuya tsakanin kungiyar ta boko haramun da kuma gwamantin kasar dake zargin wasunsu da taimakawa aiyyukan kungiyar. Mr. labaran maku dai na zaman ministan yada labaran kasar ta Najeriya kuma kakakin gwamnatin ta.
Ba zamu amince da amfani da kafafen yada labarai na waje a matsayin makamain furofagandar yan ta'adda a Najeriya. muna rokon duk kafafen yada labaran wajen dake aiyyukan su a Najeriya kar su bar kansu zama kafa ta yada matsayi na tsana da kiyayya a bangaren kungiyoyin yan ta'adda a tarayyar Nigeria.
Akalla yan jaridu biyu ne dai suka rasu sakamakon harin na boko haramun a cikin tsawon wattani 6 da suka gabata banda kuma jerin barazana iri iri ga kafafen yada labaran dama masu sana'ar ta jarida cikin kasar. Abun kuma dake kara jefa su cikin hali na gaba kura bayanta siyaki a kokarin kaiwa ga sauke nauyin sanar day an kasar dama bakin ta gaskiyar lamuran yakin day a hallaka daruruwan yan kasar kuma ke neman wucewa da sanin mahukuntanta.
Shuaibu Leman dai na zaman sakataren kungiyar Yan jaridar kasar ta Nigeria ta NUJ.
Anan Abuja dai yan jaridar da yawa na cigaba da kauracewa ofisoshi da sauran wuraren aikin nasu a wani abun dake nuna alamar tsoro game da rayuwa dama makomar su cikin yakin. To sai dai kuma kowane irin tasiri sabon matsayin ke iya yi ga aikin na jarida dai a cewar Shu'aibu leman din tsoratar day an jaridar na iya shafar cigaban tsarin demokaradiya dama makomar kasar ta Nigeria baki dayanta. Abun jira a gani dai na zaman tasirin Karin matsin lamba gay an jaridar kasar ta Nigeria da suka yi kaurin sunan fadar na albarkacin baki komai daci a kasar.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman