1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a masallacin Shi'a a Pakistan

Gazali Abdou tasawaOctober 22, 2015

Mutane kimanin 10 sun mutu a sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin 'yan Shi'a a birnin Chalgari na Pakistan a lokacin bikin sallar ashura.

https://p.dw.com/p/1GssZ
Pakistan Quetta Handery Masieh
Hoto: Banaras Khan/AFP/Getty Images

Ministan cikin gida na jihar Quetta Sarfraz Bugti ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa dan kunar bakin waken wanda wani matashi ne dan shekaru 18 da ya yi shigar tufafin mata ya tayar da bom da ke jikinsa a daidai lokacin da musulmin ke gudanar da wani taron ibada a cikin masallaci albarkacin ranar Ashura wacce take ranar farko ta linsafin kalandar muslunci da kuma ke da matukar muhimmancin ga mabiya tafarkin na Shi'a.

Ministan ya kuma ce shida daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su yara ne 'yan shekaru 10 zuwa 12. Mabiya tafarkin Shi'a dai suna da ashi 20 daga cikin dari na al'ummar kasar ta Pakistan mai kunshe da mutane miliyon 200 akasarinsu mabiya tafarkin Sunni.