1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan ƙungiyar wasa ta Togo a Angola

January 15, 2010

Gwamnatin Angola na neman yin amfani da harin da aka kai a Cabinda don ƙarfafa matsayin shugaba Jose Eduard dos Santos

https://p.dw.com/p/LXIQ
Hari kan ƙungiyar wasan ƙasar Togo a AngolaHoto: AP

Babban abin da ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon dai shi ne gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin ƙasashen Afirka da aka ƙaddamar a ƙasar Angola ranar lahadi da ta wuce tare da ba da la'akari da harin ta'addanci da wata ƙungiya ta 'yan tawaye ta kai kan ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo a lardin Cabinda, lamarin da ya sanya aka shiga saka ayar tambaya a game da matakan tsaro a gasar ƙwallon ƙafa da za a gudanar a Afirka ta Kudu nan gaba a wannan shekara. Sai dai kuma bisa ga ra'ayin jaridar Die Zeit, wannan tababar neman wuce gona da iri ne saboda Afirka ta Kudu ba ta taka wata rawa a siyasar duniya kuma bata da wasu ƙungiyoyi na 'yan tawaye. Jaridar dai ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

"Wasu daga cikin masharhanta na ƙasashen Turai na sharhi akan yankin Cabinda, kamar dai tana nan ne dab da Afirka ta Kudu, alhali kuwa tazarar dake tsakanin ƙasar Afirka ta Kudu da Cabinda ta zarce ma wadda ke akwai tsakanin Stockholm da Sarayevo a nahiyar Turai. Wani abin lura ma shi ne a sakamakon fargabar hare-haren ta'addanci a ƙasar Indiya shekarar da ta wuce, hukumar wasan ƙwallon kurket ta ƙasar ta mayar da wasan lig-lig ta ƙasar ta mayar da wasannin ma gaba ɗaya zuwa Afirka ta Kudu, lamarin da ba a taɓa ganin shigensa a tarihin wasannin motsa jiki ba."

Ita ma jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi akan harin ta'addancin wanda ta ce ga alamu ya zama tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama ga gwamnatin shugaba Jose Eduardo dos Santos, domin kuwa tana neman yin amfani da wannan dama domin ƙarfafa mulkin kama karya na shugaban ƙasar Angola. Jaridar ta ci gaba da cewa:

"A halin yanzu an shirya cewar majalisar dokokin Angola zata amince da wata sabuwar daftarin tsarin mulkin ƙasa mako mai zuwa, wanda zai kawo ƙarshen zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye da kuma soke muƙamin Piraminista. Manazarta ma na tattare da imanin cewar a yanzu za a gabatar da wasu sabbin matakai na danniya a Cabinda bayan gasar ƙwallon ƙafar ta cin kofin ƙasashen Afirka ranar 31 ga watan nan na janairu."

A wannan makon ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya kammala ziyararsa ta farko ga ƙasashen Afirka, wadda ta kai shi zuwa ƙasashen Ruwanda, Janhuriyar Demoƙraɗiyyar Kongo da Muzambik. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba sakamakon ziyarar tana mai cewar:

"A ziyarar tasa sabon ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa ya lura da inda ake samun ci gaba da kuma wuraren dake buƙatar gyara. Muhimmin abu a gare shi shi ne tabbatarwa cewa an yi amfani da kuɗaɗen taimakon da Jamus ke bayarwa a wuraren da ya kamata. Bisa ga ra'ayin ministan wannan shi ne alhakin da ya rataya a wuyansa. Domin ta haka ne zai samu ƙwarin guiwar ɗaga yawan kuɗaɗen taimakon zuwa kashi 0,7 cikin ɗari kamar yadda ake fata nan da shekara ta 2015."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal