An kai hari kussa da ƙaramin opishin jikadancin Amurika a Karashi na Pakistan
March 2, 2006Talla
Matasan ƙungiyar MEND, da ke fafatakar ƙwato yancin Niger Delta, a taraya Nigeria, sun yi belin mutane 6, daga jimmilar jami´ai 9, na ƙetare, da su ka yi garkuwa da su, tun ranar 18 ga watan day a gabata.
Wanda su ka samu belin, sun haɗa da Ba´amurike 1, da yan masar 2, 2 na Thailand, sannan mutun 1 na Phillipines.
A yanzu haka,akwai sauran mutane 3 cikin hannun su, Amurikawa 2, da dan Britania 1.
Kakakin ƙungiyar MEND, ya ce sunyi belin mutanen ba tare da karɓar diyya ba .
Matasan yankin Niger Delta, na neman a sako jagororin su, da a halin yanzu ke cikin kurkuku, kazalika dakarun gwamnati su daina kai hare hare ga al´ummomin yanki.