An kai wa 'yan sanda hari a Afghanistan
March 20, 2020Akalla jami'an tsaro 24 sun gamu da ajalinsu a kudancin Afghanistan, bayan da wasu da ake zaton 'yan Taliban sanya da kakin 'yan sanda suka bude musu wuta a lokacin da suke barci. Gwamnan lardin Zabul Rahmatullah Yarmal ya tabbatar da wannan labari, inda ma yai kara da cewa, maharan sun kwace motoci uku da makamai daga hannun 'yan sanda. Sai dai kungiyar Taliban ba ta ce uffan game da abin da ya afku ba
Wannan harin dai ya kasance daya daga cikin mafi muni a Afghanistan tun bayan da Amirka da 'yan Taliban suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Doha kan batun janyewar sojojin kasashen waje daga Afghanistan a cikin watanni 14 masu zuwa. Sai dai gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban ba su cimma daidaito kan sakin masu fafutuka da makamai 5,000 ba, wanda ke zama muhimmin mataki da Kabul ba ta amince da shi a yarjejeniyar Doha ba.