An kalubalanci Sharif kan nadin magajinsa
July 29, 2017Yan adawa sun yi watsi da nadin da Nawaz Sharif yayi wa dan'uwansa na zama Firaiminista wanda zai maye gurbinsa bayan da kotu ta sauke shi daga mukaminsa bisa laifin cin hanci.
Shugaban babban jam'iyyar adawa ta kasar Imran Khan ya kalubalanci matakin Sharif inda ya ce hakan ya sabawa tsari irin na Demokradiya, jam'iyyar adawa ta taka muhinmiyyar rawa wajen ganin kotu ta tuhumi Sharif bisa zargin yin almundahana da dukiyar kasa inda daga bisani kotu ta same shi da laiffukan cin hanci da rashawa bayan kamalla bincikenta. Daga cikin tarin zarge-zargen cin hancin da ake wa Sharif, akwai batun boye makuddan kudadde a bankunan Turai da kuma mallakar gidaje a Britaniya, zargin da tsohon Firaiministan ya sha musantawa, Sharif ya yi murabus ne bayan da kotun kolin kasar ta Pakistan ta sauke shi daga mukaminsa a wannan juma'ar.