An kama dan Ellen Johnson Sirleaf
March 5, 2019Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Monrovia babban birnin kasar Laberiya, na cewa an kama dan tsohuwar shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf tare da wasu tsoffin jami'an babban bankin kasar, bayan zarginsu da aka yi da yi wa tattalin arziki zagon kasa.
Babbar kotun Monrovia ta ce mutanen da aka zarga da buga takardun kudi ba tare da sahalewar doka ba, za su kasance a garkame ne sai har an kammala bincike a kansu.
'Yan sanda sun ce mutanen, sun buga miliyoyin kudaden kasar ne, da aka yi kiyasin za su kai dalar Amirka miliyan 16 da dubu 500.
Alkalin kotun, Kennedy Peabody, ya ce da ma dan tsohuwar shugabar ta Laberiya, wato Charles Sirleaf, na fuskantar zargin wadaka da kudaden gwamnati.