1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama daruruwan masu bore a Faransa

July 2, 2023

A Faransa, an tsaurara matakan tsaro bayan barkewar zanga-zangar nuna adawa da cin zalin da 'yan sanda ke yiwa fararen hula da ta rikide ya zuwa tarzoma.

https://p.dw.com/p/4TJhh
Hoto: Nacho Doce/REUTERS

Rahotannin sun yi nuni da cewa, a kalla mutane 486 aka kama a tsakar dare ranar Asabar. Biranen Paris da Marseille da kuma Lyon ne rikicin ya fi shafa, inda ake samun masu kwasar ganima da kuma lalata dukiyoyin jama'a. Ko da yake, ministan harkokin cikin na kasar, Gérald Darmanin ya ce an samu saukin lamura a daren Asabar sakamakon tsaurara matakan tsaro.

Firanministan kasar, Élisabeth Borne ta ce an baza jami'an 'yan sanda dubu 45 da kuma jami'an kwana-kwana a lunguna da sakon Faransar. Boren ya samo asali ne bayan harbe wani matashi dan asalin Afirka da 'yan sanda suka yi a ranar Talata.