1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

An kama fiye da masu zanga-zanga 100 a Amurka

Abdoulaye Mamane Amadou
April 27, 2024

Jami'an kwatar da tarzoma sun tarwatsa dandazon masu boren nuna goyon baya ga Falasdinawa tare da kama fiye da 100 daga cikinsu a jami'ar Boston ta Amurka a wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/4fGEN
Hoto: Joseph Przioso/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwar da ta fitar, jami'ar ta birnin Boston ta ce hukumomin na tsaro sun sallami daukacin daliban da suka nuna shaidar katinsu na karatu, tare da yin gaba da wadanda suka kasa bayyana kwararan hujjoji na kasancewarsu daliban makarantar.

Kazalika kalamun batanci da na kin jinin Yahudawa da wasu nau'ukan kalamu masu nasaba da kisan bani Yahudu da masu boren suka yi ta yadawa, na daga cikin wadanda suka kai jam'iar ga daukar matakain masu tsauri 'an zanga-zangar.

An dai share tsawon kwanaki dalibai daga jami'o'i dabam-dabam na Amurka, na bore da zanga-zangar kyamar farmakin Isra'iila a yankin Gaza, tare da nuna goyoyn bayansu ga al'ummar Falasinuwa da ke fuskantar hare-hare daga dakarun Isra'ila a kokarinta na kakkabe mayakan Hamas.