An kama hanyar warware rikicin Syria
April 4, 2018Yayin bude wani taro a kasar Turkiyya, shugabannin kasashen Turkiyya da Rasha da kuma Iran, sun jaddada aniyarsu ta hanzarta shinfida matakan kwantar da yakin nan na kasar Syria da ya dauki tswon shekaru bakwai. Taron na birnin Ankara fadar gwamnatin Turkiyya, shugaba Erdogan ya ce martaba da kuma ‘yancin Syria za su ta'allaka ne da nesanta kasar da dukkanin kungiyoyi na ta'adda.
Ana dai ganin kalaman na shugaba Erdogan a matsayin gugar zana ga kasar Amirka wadda ke goyon bayan mayakan Kurdawa, wadanda Turkiyya ke dauka makiyanta ne.
Jagabannin kasashen da za su yi zaman yini biyu ne a hukumance, za kuma su yi kokarin samar da nazariyya ta kwarai dangane da yarjejeniyar Astana ta sulhunta rikicin Syriar, musamman ma samar da tuddan mun tsira.