An kama jigon 'yan tawayen Yuganda
January 7, 2015Talla
Runduinar soji kasar Yuganda ya tabbatar da cewa mutumin da ya mika wuya ga dakarun kasar Amirka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, shi ne Dominic Ongwen, babban kwamanda a kungiyar LRA mai yakin sunkuru, wadanda suka yi kaurin suna wajen tayar da hankali.
Kakakin sojin Yuganda ya ce dan tawayen ya fara mika kai ga kungiyar 'yan tawayen Seleka, wadda ta mikashi hannun sojojin Amirka. Amirka tana taimaka wa Uganda kan yaki da 'yan tawayen kungiyar LRA wajen farautar shugaban 'yan tawayen da ke yakin sunkuru Joseph Kony.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe