An kama maharan Gabon
December 18, 2017Talla
Rundunar 'yan sanda a kasar Gabon ta cafke wadanda ake zargi da raunata ma'aikata biyu 'yan kasar Denmak a wani yunkurin nuna adawa da ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'la da shugaba Donald Trump na Amirka ya yi. Su dai wadanda aka kama din mafi yawan su 'yan kasuwa ne a babbar kasuwar birnin Libreville da ke kasar ta Gabon kamar yadda Alain-Claude Bilie kakakin gwamnatin kasar ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP .
Ya kuma kara da cewar wanda ya kai harin mai kimanin shekaru 53 'dan Nijar ne kuma ya bayyanawa jami'an tsaro cewar ya aikata wannan ta'adda ne sakamakon sanarwar da shugaba Trump ya yi a kan birnin Kudus.