1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama mayakan da suka fille kan 'yan jarida

Ramatu Garba Baba
February 9, 2018

Rundunar hadin gwiwa da Amirka ke jagoranta ta ce ta kame wasu mayakan kungiyar IS biyu 'yan asalin kasar Britaniya da suka yi kaurin suna a fille kan mutane bayan sun yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/2sO4i
Dan jarida James Foley
Hoto: dapd

A sanarwa da rundunar ta fitar ta bakin kakakinta Kanal John Thomas ya ce, an kama El Shafee El Sheikh da Alexander Amon Kotey a watan Janairun da ta gabata a gabashin kasar Siriya.

Ya kara da cewa mayakan jihadin biyu na daga cikin mambobin kungiyar ta IS da suka kama tare da fille kanun wasu mutane akalla goma bayan da suka yi garkuwa da su a Siriyan, cikin wadanda aka fillewa kan a wancan lokacin akwai 'yan jaridan Amirka James Foley da Steven Sotloff da kuma wani mai aikin agaji Peter Kassig.

Kakakin rundunar sojin,  ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan mayakan biyu ya kuma ce wannan wata babbar nasarar ce ga Amirka da kuma iyalan wadanda aka kashen.