1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama tarin makamai a Lagos

November 24, 2010

Jami'an tsaro a Najeriya sun sake kama bindigogi da kayan soji, a tashar jiragen ruwan Lagos.

https://p.dw.com/p/QGyp
Taswirar Najeriya, ke nuna Lagos

A Najeriya hukumomin tsaron ƙasar sun kama wasu makamai a tashar jiragen ruwan Lagos. Kayakin da dukkanninsu waɗanda soji ke amfani da sune, an kuma kama su ne bayan makwanni da hukumomi a Najeriya suka kama wasu makaman a tashar jiragen ruwan dake Lagos. Kakakin rundunar sojin ruwa Kaptin Kabiru Aliyu, shine ya shaida wa manema labarai kamun makaman. Kaptin Kabiru Aliyu yace makaman sun haɗa da ƙanan bindigogi da harsasai barkatai da rigunan da harsashi baya hudawa da takalman sojoji. Duk kayakin an zuba su ne a wata motar da aka yiwa pentin kore, na alamar soji, kana Kaptin Aliyu yace akwai motocin sulke guda takwas da akayiwa pentin soji duk a cikin makaman da suka kama a yau, waɗanan kuwa duk kayakin da aka haramta shigowa da su. Izuwa yanzu Kaptin Aliyu yace an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a shigo da kayakin, sai dai bai bayyana ko daga wace ƙasa ce, kayan soji da makaman da aka kama suka fito.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu