1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wasu kusoshin hukumar FIFA

Gazali Abdou TasawaDecember 3, 2015

Ana zargin Juan Angel Napout dan kasar Paragai da kuma Alfredo Hawit Banegas dan kasar Honduras mataimakan shugaban hukumar a bisa zarginsu da karbar hanci na miliyoyin Dala.

https://p.dw.com/p/1HHE9
Joseph Blatter und Issa Hayatou
Hoto: picture-alliance/dpa/Messara

Hukumomin shari'ar kasar Switzerland sun bada sanarwar kama bisa umarnin kasar Amirka wasu mataimakan shugaban hukumar FIFA su biyu da suka hada da Juan Angel Napout dan kasar Paragai da kuma Alfredo Hawit Banegas dan kasar Honduras.

Amirka na zargin mutanen biyu ne da karbar hanci na miliyoyin Dala a cikin bayar da kongilar tallace-tallace na nuna wasannin latin Amirka da kuma na cin kofin kwallon kafa na duniya.

Sai dai mutanen biyu sun bayyana adawarsu ga matakin neman mikasu ga kasar ta Amirka. Amma shugaban riko na Hukumar ta FIFA Issa Hayatou ya ce hukumar za ta ci gaba da bada hadin kai ga hukumomin shari'ar kasar ta Amirka:

Kamen wadannan kusoshi na Hukumar ta FIFA ya zo ne a daidai lokacin da komitin zartarwarta ya soma wani zama a cibiyar hukumar da ke a birnin Zurich da nufin fito da shawarwarin kawo gyara da zai maido da martabar hukumar ta FIFA.