An kama 'yayan Mubarak na Masar guda biyu
April 13, 2011Hukumomin riƙon ƙwarya na Masar sun cafke biyu daga cikin 'yayan hamɓararren shugaban ƙasa Hosni Mubarak, bisa zarginsu da ake yi da bayar da umurnin murƙushe wasu daga cikin masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati na kwanakin baya. kana ana zarginsu da laifin cin hanci da rashawa da kuma sama da faɗi da dukiyar ƙasa. Shi ma dai mahaifin nasu wato Hosni Mubarak, an tuhumeshi da laifin karkata aƙalar baitilmali, tare da musguna wa jama'a lokacin da suka nemi da ya sauka daga karagar mulki.
Sai dai hamɓararen shugaban mai shekaru 82 da haihuwa, ba zai samu damar hallara a gaban kotun da ke birnin Alƙahari ba, saboda kwantar da shi da aka yi a asbitin birnin Char el-Cheikh sakamakon ciwon bugun zucciya da ya ke fama da shi. Hukumomin mulkin sojen na Masar sun bayyana aniyarsu na gurfanar da duk dangi Mubarack da kuma na hannun hamɓrarren shugaban da ake zargi da hallarta kuɗin haramun.
Amma kuma 'yan ƙasar da suka aiwatar da juyin juya hali sun zargi gwamnatin riƙon ƙwarya da jinkiri wajen kawar da na hannun daman Mubarak daga madafun iko tare da gurfanar da su gaban ƙuliya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar