An kammala ganawa tsakanin Merkel da Sarkozy
July 16, 2007Daruruwan ma´aikatan kamfanin kera jiragen saman samfurin Airbus ne suka hallara a babban zauren harhada katafaren jirgin saman nan samfurin Airbus A 380. Wahalhalun da aka fuskanta dangane da wannan jirgin sama ya janyo sabanin ra´ayi tsakanin Jamus da Faransa. Daga bisani ya bayyana a fili cewa tsarin shugabanni biyu ke hana kamfanin ci-gaba. Saboda haka yanzu a soke wannan tsari. A jawabin da ta yi a gaban ma´aikatan kamfanin SGJ Angela Merkel ta yi bayani game da wani yanayi na kaduwa.
Merkel:
“Na ji dadi yadda na sadu da ku a yau, wato da yawa daga cikin ma´aikata Faransawa da Jamusawa. Hakan shaida ce game da kyakkyawar zamantakewa tsakanin Jamusawa da Faransa a cikin garin Toulouse, wadda sau da yawa labarinsa kadai muke ji.”
Da farko daga gun ´yan jarida ma´aikatan suka labarin cewa za´a yiwa kamfanin wani sabon fasali. Wato Louis Gallois dan kasar Faransa wanda kawo yanzu yake daya daga cikin shugabannin biyu na Airbus, shi ne zai zama shugaban kamfanin kera jiragen sama da makamai na Turai wato EADS. Yayin da takwaransa na Jamus Thomas Enders zai jagoranci kamfanin Airbus shi kadai. Enders mai shekaru 48 ya nuna gamsuwa inda ya ce sabon mukaminsa na da muhimmanci ga uwar kamfanin wato EADS.
Enders:
“Makomar kamfanin ta dogara akan kyakkyawar makomar Airbus. Hakika babu karin abin da za´a iya yiwa kamfanin saboda haka na ke maraba da wannan zabi.”
Aikin sa zai kasance aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun kamfani wanda ake yiwa lakabi da power 8 wanda ya tanadi rage yawan ma´aikata. Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya ce dukkan bangarorin biyu na bukatar yin aiki tukuru, inda ya kara da cewa za´a rika yin bayayya na mukaman bayan shekaru 5-5.
Sarkozy:
“Bayan wannan wa´adi Bafaranse zai shugabanci majalisar gudanarwa. Ana iya bawa Arnaud Largadere wannan mukami idan yana so. Ina gode masa da gudunmawar da ya bayar wajen cimma wannan daidaito.”
Ra´ayoyin Merkel da Sarkozy sun zo daya akan ´yancin babban bankin Turai. Da farko dai shugaban Faransa dai na zargin cewa karfin takardun kudin Euro ne musababbin matsaloklin tattalin arzikin da kasarsa ke fama da su, saboda ya nuna bukatar gabatar da manufofin tattalin arziki bisa manufa.
Wakilan kungiyoyin kwadago a hedkwatar ta Airbus sun soki wannan maslaha suna masu cewa soke tsarin shugabanni biyun ba zai kawo karshen angizon wasu kasashe a cikin kamfanin ba.