An kammala taron samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
March 19, 2010An kammala taron samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da aka gudanar a birnin Moscow tare da kira ga Israila da Palasɗinawa su taimaka wajen samun zaman lafiya cikin watanni 24. A jawabin daya gabatar Ban ki-moon yace - muna kira ga Israila da Palasɗinawa dasu hinmatu wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin kamar yadda yake kafin shekarar 1967 domin samun zaman lafiya tsakanin su da kuma maƙwabtan su. Wannan taro yazo ne mako guda bayan da Israila ta bada sanarwar cigaba da faɗaɗa matsugunan yahudawa a yankun Palasɗinawa.Taron wanda Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ɗauki nauyin gudanarwa, ya samu halartar Babban Sakataren Majalisar ɗinkin duniya Ban ki-moon da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da kuma babbar Jami'ar harkokin wajen ƙungiyar Turai Catherin. Ganawar manyan jami'an diplomasiyar yazo ne a dai dai lokacin da Palasɗinawa suka harba wani roka daga yankin Gaza, ita kuma Israila ta maida martani da hare haren jiragen sama a tsakan dare.
Mawallafi:Babangida JIbril
Edita:Abdullahi Tanko Bala