An kara wa´adin daurin talala da ake yi wa Aung Suu Kyi a Burma
November 27, 2005Talla
Gwamnatin mulkin sojin kasar Burma ko Myanmar ta tsawaita daurin talala da take yiwa shugabar ´yan adawa Aung San Suu Kyi da shekara daya, inji majiyoyin ma´aikatar harkokin cikin gida a birnin Rangun. Kafofin yada labarun kasar sun ce wakilan gwamnati na yawaita gudanar da bincike a gidan matar wadda ta taba samun kyautar Nobel ta zaman lafiya. Kamar dai jam´iyarta ta National Democratic League, ita ma kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa wato Amnesty International sun yi kira da a sako Suu Kyi. Tun kimanin shekaru 15 da suka wuce aka fara yi mata daurin talala a gidan ta dake birnin Rangum.