Somaliya: An kashe mayakan al-Shabaab 37
November 20, 2018Talla
Babu rahotannin asarar rayukan fararen hula yayin artabun tsakanin dakarun gwamnati da mayakan. Dakarun kawancen Amirka da sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka AU tare da sojojin Somaliya na ayyana cin galaba kan kungiyar al-Shabaab.
Kungiyar al-Shabaab ta sha kaddamar da hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro da gine-ginen gwamnati da zimmar kafa daular musulunci a Somaliya.