SiyasaAfirka
'Yan ta'adda sun halaka sojojin Mali
March 5, 2022Talla
Wani harin mayaka masu ikirarin jihadi a wani barikin soji da ke tsakiyar kasar Mali ya yi ajalin rayukan sojoji 27 da kuma halaka 'yan ta'adda 47. Rundunar sojin Mali wace ta sanar da haka a cikin wata sanarwa, ta ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Jumma'a. Ta kuma ce artabu ne da ya raunata sojoji da 'yan ta'adda da dama.
Wata majiya ta sojin Faransa da ba ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran na AFP sunanta ba, ta ce adadin sojoji da 'yan ta'adda da suka rasa rayukansu ma zai iya zarta alkaluman da sojojin Mali suka sanar.