An kashe wasu 'yan ƙasashen waje a Pakistan
June 23, 2013Hukumomin tsaro sun ce mutanen sun buɗe wuta ne a kan baƙin da ke a wani Otel ɗin inda suke da masabki.
Gidan talabijan na ƙasar na Pakistan PTV ya ambato wani babban jami'in 'yan sanda Ali Sher na mai cewar a cikin waɗanda suka mutu a kwai 'yan ƙasashen Yukren guda biyar da ' yan China guda uku da ɗaya ɗan Rasha. Jami'in dai ya ƙara da cewar maharan sun kai harin ne a cikin dare lokacin da mutanen ke yin barci. Garin dai na Gligit-Baltisan da ke kan iyaka da China da Kuma Cachmire, ana ɗaukar shi a matsayin wani wuri mafi kwanciyar hankali a Pakistan.To sai dai a 'yan shekarun baya baya nan ya kasance wata cibiya da masu kishin addini ke kai hare-hare galibi a kan tsiraru 'yan Shi'a.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu