1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun mutu a Aljeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
January 2, 2021

Sojojin biyu sun mutu a yayin da 'yan ta'adda hudu suka hallaka a sakamakon gumurzun da suka yi a lardin Tipaza na yammacin babban birnin Aljeriya

https://p.dw.com/p/3nScO
Symbolbild Algerien Geiselnahme Islamischer Staat Franzose
Hoto: picture-alliance/AP

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriyar ta ce sojojinta sun gamu da ajalinsu ne a yayin wani samamen da suka kai don kakkabe 'yan ta'adda masu fatutikar jihadi da makamai da suka yi kaurin suna a kasar tubayan yakin basasar da ta fuskanta a 1992 zuwa 2002.

Sai dai rundunar tsaron kasar, ta ce ta samu nasarar hallaka mayakan jihadi hudu, tare da kwatar tarin makamai masu sarrafa kansu da bindigogi, kana tuni shugaban kasar ya aike da sakon ta'aziyarsa ga iyalan sojan da suka rigamu gidan gaskiya.

Ko a ranar 17 ga watan jiya, rundunar tsaron Aljeriya, ta ce ta kama wanio gursunkumin dan ta'adda da ta kira mai hadarin gaske a yankin Jijel da ke Arewa maso gabashin birnin Algers.