An kashe 'yan jarida 110 a shekara ta 2015
December 29, 2015Kungiyar kare 'yancin aikin jarida ta kasa da kasa ta Reporteurs Sans Frontiere(RSF) ta ce 'yan jarida 110 aka halaka a cikin hanyar gudanar da aikinsu a wannan shekara ta 2015 da ke shirin karewa.
Kungiyar ta RSF ta bayyana wadannan alkalumma ne a cikin rahotonta na shekara-shekara da ta wallafa a wannan Talata.
Kasar Iraki ta kasance a sahun gaban kisan 'yan jaridar a shekarar ta bana da mutuwar 'yan jarida 11 kasar Siriya na bi mata da mutuwar 'yan jarida 10 ,Faransa na a matsayin ta uku da mutuwar 'yan jarida takwas.
Alkalumman na shekarara ta 2015 sun sha gaban na shekara ta 2014 inda aka hallaka 'yan jarida 66 a kan hanyar gudanar da aikin nasu.
A kan haka ne ma Kungiyar ta RSF ta bayyana bukatar ganin ba tare da bata lokaci ba an nada wani wakilin musamman na kare 'yancin 'yan jarida a Majalisar Dinkin Duniya.
'Yan Jarida 787 ne a cewar kungiyar ta RSF aka hallaka kan hanyar aikinsu daga shekara ta 2005 zoke yau.