1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan ta'adda a Masar

November 4, 2018

Jami'an tsaro a Masar sun kashe wasu 'yan bindiga da ake zarginsu da kashe wasu mabiya a ranar Juma'ar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/37diP
Ägypten Protest
Hoto: picture-alliance/AA/Stringer

Hukumomin na Masar ne suka tabbatar da kisan 'yan bindiga su 19 wadanda ake zargin su ne kashe Kiristoci Kibdawa a ranar Juma'ar da ta gabata a yankin kudancin birnin Alkahira.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce an bi sawun 'yan bindigar ne har zuwa maboyarsu da ke a garin Minya, inda suka aikata aika-aikar.

Haka nan ma'aikatar ta wallafa wasu hotunan gawarwakin 'yan bindigar, wadanda bayanai suka ce sun maida martani da bindigogi lokacin da jami'an tsaro suka mamaye su.

Harin na ranar Juma'a dai, shi ne na biyu da ake yi kan masu zuwa ibada a cocin St. Samuel, kuma ko a watan Mayu ma, wasu 'yan ta'addan sun kashe Kibdawan 29.