An kawo ci-gaba inji Namadi Sambo
September 18, 2013Ya zuwa badi dai a cewar mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo kuma jagoran samar da wutar kasar. 'Yan Najeriya suna shirin ganin daban a cikin harkokin wutar da suka share shekara da shekaru suna fatan kawo karshen matsalar, amma kuma suka kare ba tare da samun ci -gaba ba. Akalla megawatt 9000 ne dai a cewar Arc Namadi Sambo, tarayyar ta Najeriya ke shirin samu a badin, abun kuma da a cewar sa ya kama hanyar kaddamar da kasar cikin tarihin kawo karshen matsalar da ake ta'allakawa da koma bayan kasar na lokaci mai tsawo.
Tuni dai Tarayyar Najeriyar a cewar mataimakin shugaban ta kai ga cefanar da daukacin cibiyoyin samar da wutar kasar, sannan kuma ta na shirin amfani da kudin wajen sake ginin wasu sababbi na ruwan saman da za su baiwa kasar karin megawatt 5000 cikin wasu shekaru biyar masu zuwa.
Babbar takadama cikin kasar ta Najeriya ya zuwa yanzu dai na zaman na tsadar ayyukan kwangilar sababbin cibiyoyin wutar kasar da kafafen yada labarai, suka ce na zaman mafi tsada a duniya amma kuma Sambo ya kira zuki ta Malle.
Ko bayan batun wutar da ya gagari kundila dai, a cewar mataimakin shugaban Najeriyan, lokaci ya iso na tsalen murna a bangaren al'umar arewacin kasar, da a baya suka sha korafin nuna wariya wajen gina filayen jiragen saman kasar.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin da ta ce tana shirin kara fadin filin jirgin saman Aminu Kano da ke birnin Kano, ta kuma ce ta bar izini ga jiragen sama na Emirate Airline na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Turkish Airline na Turkiya za su fara sauka da tashi daga birnin Kano dama filin jirgin sama na Abuja.
An dai share tsawon lokaci ana kace-nace a tsakanin gwamnatin kasar da yar uwarta da ke jihar Kano game da batun hanawa manyan jirage na duniya zuwa Kano dama sauran sassa na arewacin Najeriya.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman