An kebe wasu sojoji a Liberiya saboda Ebola
October 11, 2014Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa ana sanya idanu ga wasu ma'aikata 41 da ke aiki karkashin ayyukan wanzar da zaman lafiya ciki kuwa har da sojoji 21, bayan da aka gano daya daga cikin ma'aikatan na kasa da kasa na ya sake harbuwa da kwayoyin wannan cuta ta Ebola da ya kai wadanda ke aiki karkashin shirin suka zama su biyu.
Wannan mataki dai na iya zama na rigakafin kaucewa sake bazuwar wannan cuta a tsakanin ma'aikatan. Ma'aikatan dai na Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a wannan kasa ta Liberiya a ranar jumaa sun bayyana cewa cikin mutanen da suka yi mu'amula da ma'aikacin nasu tun da fari babu wanda ke nuna alamar ya kamu da cutar sai dai za su ci gaba da sanya idanu a kansu har tsawon kwanaki 21 ko da alamun cutar za su bayyana.
Bayyanar annobar wannan cuta dai ta yi sanadin mutuwar mutane 4,000 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana.