An kori rasha daga majalisar Turai
March 16, 2022Talla
Tun a ranar Talata majalisar ta kada kuri'ar fitar da Rasha daga cikinta kafin daga bisani a wannan Laraba kwamitin amintattu na majalisar ya amince da matakin a yayin wani taron gagagwa da ya gudanar.
Rasha da ta kasance mamba a majalisar Turai tun a shekarara 1996, sai dai ta sanar da ficewa cikin majalisar bayan da ta zargi kasashen da yi mata barazana.
Manazarta dai na ganin matakin fitar da Rashar daga majalisar ka iya jefa 'yan kasar cikin wani garari na rashin samun cikakkiyar kariya daga kotun kare hakin bil'Adama ta Turai.
Wannan ne karo na biyu a tarhin Turai da wata kasa ke ficewa daga majalisar, tun bayan makamancinsa da Girka ta yi a shekarar 1969, kafin ta sake dawowa a shekarar 1974.