1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kori shugaban jam'iyyar Conservative kan haraji

Ramatu Garba Baba
January 29, 2023

Firaminista Rishi Sunak ya kori Nadhim Zahawi daga shugabancin jam'iyyarsa ta Convervative kan laifin kin biyan kudin haraji a lokacin da ya ke rike da mukamin minista.

https://p.dw.com/p/4Mq44
Nadhim Zahawi
Nadhim ZahawiHoto: Christine Ongsiek/Avalon/Photoshot/picture alliance

Firaminista Rishi Sunak na Britaniya ya dauki matakin korar shugaban jam'iyyarsa ta Convervative ne, bayan da bincike ya tabbatar da zargin da ake wa Mista Nadhim Zahawi da laifin kin biyan kudin haraji a lokacin da ya ke rike da mukamin ma'aji na baitulmanin kasar. Sai dai Zahawi ya musanta laifin, yana mai cewa, akwai kuskuren da ya tafka amma bai yi da niyyar kaucewa biyan harajin ba.

Firaiminista Sunak ya ce, laifi ne da ba za a lamunta ba domin ya saba wa ka'idojin aikin Britaniya. Zahawi shi ya rike mukamin ministan kudi a lokacin da Britaniya ke tsakiyar fama da rikicin siyasa a bara.