An kunce bam na lokacin yakin duniya na biyu a Hamburg
October 13, 2024Hukumar jami'an kwana-kwana ta Jamus ta gudanar da gagarumin aiki na kunce wani bam tun na lokacin yakin duniya na biyu da aka gano a wata anguwa da ke birnin Hamburg a daren ranar Asabar.
An tilastawa duban mazauna anguwar da aka gano bam din barin gidajensu tare da rufe gidajen cin abinci da na raye-raye na anguwar da ake kira Sternschanze a lokacin da ake gudanar da wannan aiki mai matukar hadari. Har ila yau gano bam din ya kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen kasa mausamman a tashar jiragen kasa ta Sternschanze wadda ke samun cunkoson jama'a a duk karshen mako.
Karin bayani: Barnar ababen fashewa a Jamus
An gano bam din a lokacin da ake aikin gini a harabar wata makarantar firamare, kuma a cikin wata sanarwa da hukumar jami'an kwana-kwana ta fidda da sanhin safiyar Lahadi ta ce an kunce bam din ba tare da an samu wata matsala ba bayan share sa'o'i kusan shida ana aiki.