An kwantar da shugaban Aljeriya Bouteflika a wani asibitin birnin Paris
November 27, 2005Ma´aikatar harkokin wajen Faransa ta ce an hanzarta kai shugaban Aljeriya Abdelaziz Bouteflika wani asibitin birnin Paris bisa wasu dalilai na rashin lafiya da ba a bayyana ba. Kakakin ma´aikatar ya ki yayi karin bayani baya ga tabbatar da rahoton cewa har yanzu shugaban na Aljeriya mai shekaru 68 na nan a baban birnin na Faransa. Wata majiyar gwamnati ta ce ana yiwa Bouteflika jiya ne a asibitin sojin Val-de-Grace dake birnin Paris. A wannan asibiti aka kwantar da shugaba Jaques Chirac tsawon mako guda a cikin watan satumba. Ofishin Bouteflika ya ce shugaban na Aljeriya na fama da wata matsala ce a ciki musamman bayan hadiye abinci to amma ba wata abar damuwa ba ce. A bara an kwantar da shugaban Falasdinawa marigayi Yasser Arafat a wani asibitin sojin Faransa dake wajen Paris sakamakon wani rashin lafiya da hukumomin Falasdinu suka ce mura ce. To amma daga baya majiyoyin asibiti suka ce mummunan ciwon jini, wanda kuma yayi ajalinsa a ranar 11 ga watan nuwanban shekara ta 2004.