1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada sabon firaminista a Burkina Faso

Abdoulaye Mamane Amadou Ahmed Salisu
October 22, 2022

An nada lauya mai zaman kansa Appolinaire Joachim Kyelem de Tembela a matsayin sabon firaminstan gwamnatin rikon gwarya ta mulkin soja a Burkina Faso, kwanaki bayan juyin mulki.

https://p.dw.com/p/4IXk8
Burkina Faso | PK Ibrahim Traore
Hoto: AA/picture alliance

Sabon shugaban majalisar koli ta gwamnatin mulkin soji ta rikon kwarya a Burkina Faso ya nada Appolinaire Joachim Kyelem de Tembela a matsayin wanda zai tafiyar da majalisar ministocin kasar.

Kusa a fannin dokokin sha'ara kuma lauya mai zaman kansa, Appolinaire Joachim Kyelem de Tembela ya yi kaurin suna wajen caccakar tsohuwar gwamnatin da ta shude kan kasawa a fannin tabbatar da tsaro.

Mai shekaru 64 a duniya Kyelem de Tembela ya samu sahalewar sabon shugaban kasar Captine Ibrahim Traoré ne a jiya bayan da ya saka hannu kan kudrin da ya nada shi da aka karanta a kafar talabijin din kasar, sai dai masana na cewa babban kalubalen da ke a gabansa sun hada da magance matsalolin tsaro da suka janyo gwamnatin sake kwarce mulki.