Jamus ta yi sabuwar ministan tsaro
July 17, 2019Shugabar Gwamantin Jamus Angela Merkel ta zabi Annegret Kramp-Karrenbauer shugabar Jam'iyyar CDU a matsayin sabuwar ministar tsaron kasar ta Jamus domin maye gurbin Ursula von der Leyen wacce Majalaisar Dokokin Turai ta zaba a matsayin sabuwar shugabar Kungiyar Tarayyar Turai.
Majalisar Dattawa ta Bundesrat ce ta sanar da wannan nadi a cikin wata sanarwa da ta fitar a jyia Talata. A yau ne a nan gaba kadan a wannan Laraba mataimaki shugaban majalisar wakilan ta Bundesrat zai kaddamar a birnin Berlin da sabuwar ministar da ake yi wa lakabin AKK.
Kramp-Karrenbauer 'yar shekaru 56 a duniya ta soma yin tasiri ne a fagen siyasar kasar ta Jamus bayan da a watan Disemban da ya gabata aka zabe ta a matsayin sabuwar shugabar Jam'iyyar CDU bayan da Merkel ta sanar da ba za ta sake tsayawa takarar neman shugabancin gwamnatin kasar ba a zabe mai zuwa.