1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada Sarkin Ingila bayan shekaru 70

May 6, 2023

An nada Sarki Charles na III a matsayin Sarki a Burtaniya inda ya gaji mahaifiyarsa Elizabeth ta II wadda ta rasu a bara.

https://p.dw.com/p/4Qzaq
Nadin Sarki Charles III a birnin Landan
Hoto: Jonathan Brady/PA/AP/picture alliance

A wannan Asabar din ne aka gudanar da bikin nadin Sarki Charles na III a matsayin Sarki a Burtaniya, inda ya gaji mahaifiyarsa Elizabeth ta II wadda ta mutu a bara.

Wannan ne nadi a hukumance da aka yi Burtaniya ke gani tun bayan wanda aka yi a ranar 2 ga watan Yunin shekarar 1953, wato kusan shekaru 70 da suka gabata.

Manyan baki daga sassa daban-daban na duniya sun kasance a Cocin Westminster Abbey da ke birnin Landan, inda suka shaida nadin Sarki Charles na III da misalin karfe 11:02 agogon GMT.

Firaministan Burtaniyar Rishi Sunak da sauran tsoffin Firaministocin kasar su bakwai sun kasance a wajen bikin nadin.

Sarki Charles na III dai ya ce bai zama sarki don mutane su rika yi masa bauta ba, domin shi ne zai yi musu.