Yuganda: Bincike kan kisan mutum 100 a masarauta
November 28, 2018Talla
Harin na watan Nuwambar shekarar 2016, da sojoji suka kai kan sarkin na Rwenzururu, wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaba Yoweri Museveni, ya ja hankalin duniya inda har ya zuwa wannan lokacin ake kira na ganin an hukunta wadanda ke da hannu a aika-aikar.
Amirka da kungiyar tarrayar Turai da kuma kungiyar Human Rights sun ce gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace kan jami'an tsaron da ake zargi ba, batu ne da suke ganin bai kamata a ce an tsaya ana jan kafa ba. Akwai bukatar a dauki matakin kwatarwa jama'a da lamarin ya shafa hakkinsu inji sanarwar da suka fitar.
Yara kanana 15 na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a yayin musayar wuta da aka yi a tsakanin sojoji da kuma mukarraban sarkin.