1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Samia Suluhu Hassan mace ta farko shugabar kasa

Abdoulaye Mamane Amadou
March 19, 2021

Kwanaki biyu bayan mutuwar shugaban kasar John Magufuli, an rantsar da mataimakiyar shugaban kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, a matsayin sabuwar shugabar kasa.

https://p.dw.com/p/3qs3z
Tansania Daressalam | Amtseinführung neue Präsidentin Samia Suluhu Hassan
Hoto: Stringer/REUTERS

Mai shekaru 61 kuma Muslma, Misis Hassan ta kasance mace ta farko ta rike mukamin shugaban kasar Tanzaniya a tarihi, domin cike gzurbin wa'adin mulkin marganyi Magafuli da zai kawo karshe a shekarar 2025. Agaban alkalan kotun tsarin mulkin Tanzaniya, sabuwar shugabar ta karbi rantsuwa da alkur'ani mai girma, ta ce "Na yi alkawarin yin gaskiya tare da bin doka da kare kundin tsarin mulkin kasar Tanzaniya." Sabuwar shugabar ta kuma sha alwashin dorawa inda mulkin maragayi Magufuli ya tsaya don ci gaba da inganta rayuwar 'yan kasar a yayin takaitaccen jawabinta a bainar jama'a.