Nijar: Bude zaman sabuwar majalisa
April 7, 2021Da yake rantsuwar kama aikin, sabon firaministan na Jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya sha alwashin yin aiki cikin mutunta dokokin kasa tare da kama aiki gadan-gadan, musamman ganin yadda al'ummar Nijar suka zuba masa ido domin suga yadda sabuwar majalisar ministocin gwamnatin tasa za ta kasance.
Karin Bayani: Ra'ayin 'yan Nijar kan nadin sabon firaminista
Ya dai sha rantsuwar ne a gaban 'yan majalisar dokoki da wasu manyan baki daga ciki da wajen kasar da suka hada da jakadun kasashen waje a Jamhuriyar ta Nijar.
'Yan majalisar dokoki na bangaren adawa sun halarci bude zaman majalisar na wannan rana. Sai dai kuma sun fice baki dayansu a lokacin da ake shirin rantsar da sabon firamnistan.
Karin Bayani: Bazoum zai yi aiki da kasashe makwabta
Bikin bude zaman farko na majalisar dokokin kasar ta Nijar ya samu halartar wata babbar tawagar 'yan majalisa daga makwabciyar kasa Tarayyar Najeriya. Majalisar dokokin ta Nijar za ta kwashe watanni uku tana wannan zama, inda baya ga kafa kwamitocinta za ta kuma yi nazari da sanya hannu kan wasu dokoki da gwamnati za ta gabatar a gabanta.