An rantsar da shugaban Ƙasar Pakistan
November 29, 2007Talla
An rantsar da shugaban Pakistan Parvez Musharraf a matsayin shugaban farar hula wanda zai yi mulki na tsawon shekaru 5,kwana guda bayan ya tuɓe kakinsa na soja.Wanda ya rantsar da shi kuwa shine babban alkalin alkalan kasar Abdul Hameed Dogar wanda aka naɗa a ranar uku ga watan Nuwamba a lokacin da tsohon janar ɗin ya kafa dokar ta ɓaci tare da korar yawancin manyan alkalan ƙasar ta. Amurka da jamiyun siyasa na Pakistan suna ci gaba da matsawa Musharraf lamba da ya ɗage dokar kafin zaɓen ranar 8 ga watan Janairu.