SiyasaJamus
Kawancen jam'iyyun Jamus ya amince da kafa gwamnati
December 7, 2021Talla
Yarjejeniyar na zama mataki na karshe kafin ranar Laraba, inda Majalisar Dokoki ta Bundestag za ta tabbatar da Olaf Scholz na jam'iyyar SPD a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus a hukumance, matakin da zai kawo karshen wa'adin shugabancin Angela Merkel na tsawon shekatru 16.
Jagorar jam'iyyar The Greens Annalena Baerbock wace ta samu mukamin ministan harkokin wajen Jamus da jagoran jam'iyyar FDP Christian Lindner da shi kuma ya samu mukamin ministan kudi, sun jinjina wa hadin kan da suka samu daga jam'iyyar SPD wace ke da kaso mai tsako a sabuwar gwamnatin ta Jamus.